Kotun daukaka kara ta haramtawa Aleiro da Abdullahi takarar sanata a Kebbi

0
85

Kotun Daukaka Kara da ke Sakkwato ta hanawa tsohon Gwamnan Kebbi, Sanata Adamu Aleiro da tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi takarar Sanata a Kebbi ta Tsakiya da Kebbi ta Arewa.

Alkalin kotun, Muhammad Shu’aibu a hukuncin da ya zartas a yau Laraba wanda dukkanin alkalan suka amince ya yi watsi da karar da Aleiro da Abdullahi suka shigar a inda suka bukaci kotun ta tabbatar da su a matsayin halastattun ‘yan takarar PDP.

A hukuncin ta, kotun ta tabbatar hukuncin Kotun Tarayya da ke Birnin Kebbi da cewar Haruna Sa’idu Dandilo ne halastaccen dan takarar jam’iyyar PDP a Mazabar Kebbi ta Tsakiya a 2023. Haka ma ta tabbatar da Sani Bawa Argungu a matsayin dan takarar Sanata a Kebbi ta Arewa.

Sa’idu ya shigar da kafar ne tun farko a Kotun Tarayya yana kalubalantar sake gudanar da sabon zaben fitar da gwani da jam’iyyar PDP ta gudanar wanda aka bayyana tsohon Gwamna, Aleiro a matsayin wanda ya yi nasara.

Dan takarar, ya yi karar Aleiro, wanda yanzu haka shine Sanata a mazabar da jam’iyyar PDP da kuma Hukumar Zabe saboda gudanar da sabon zaben fitar da gwani a Kebbi ta Tsakiya wanda a cewarsa sabon zaben fitar da gwanin ya sabawa kundin dokar zabe ta 2022. Ya ce yana raye, bai jaye takara ba, don haka ba bisa ka’ida aka canza sunansa na, wanda a kan hakan Kotun Daukaka Kara a yau ta tabbatar da hukuncin farko ta hanyar watsi da karar.