Jarumin na zargin fitaccen marubuci Aliyu Imam Indabawa, da yi masa kazafi da bata masa suna a wani rubutu da ya yi a kansa, tare da neman ya biya shi wasu kudi.
A hirarsa da Aminiya, jarumin ya ce, Indabawa ya kirkiri karyar cewa jarumin na kokarin lalata da wata yarinya budurwa da ake shirin yi mata aure.
Sannan kirkiri sakonnin WhatsApp yana yadawa a fakofin sada zumunta a matsayin hirarsa da yarinyar, wanda har wasu jaridu na intanet suka yada.
A cewarsa, kafin ya yi masa kazafin sai da marubucin ya kira shi a waya ya nemi ya ba shi wasu kudi, ko kuma ya tozarta shi.
“Yanzu haka dai yana hannu can ofishin ’yan sanda suna gudanar da bincike kan lamarin domin ya ce sa shi aka yi.
“Tun da sa shi aka yi, ka ga yanzu zai fadi ko wane ne, sannan idan an gama biciken za a mika mu kotu,” in ji Jarumi Sahir Abdul.
Jarumin ya kuma ce, ya dade na yana neman marubucin bayan ya yi masa kazafin, bai shiga hannu ba sai a cikin ’yan kwanakin nan.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, sun gayyaci marubucin ne, suna kuma gudanar da bincike.