Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya IPMAN ta dora alhakin karancin man a Lagos da Abuja da sauran jihohin kasar kan tsadar farashin Dala da kuma yadda Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya gaza sakin wadataccen man.
Akwai dogayen layukan ababen hawa a sassan Lagos da Abuja duk da cewa, ana sayar da lita guda akan farashin Naira 180 ko ma fiye da haka.
Matsalaar ta karancin man ta tilasta wa direbobin motocin haya tsauwala kudin mota ga fasinjoji.
Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar IPMAN, Chief Ukadike Chinedu ya ce, manyan jiragen ruwa na shigo da man fetur cikin Najeriya ta kan iyakar Lagos, yayin da kananan jiragen ruwa ke kai man zuwa tashoshin jiragen ruwa na Lagos da Warri da Fatakwal da dai sauransu.
Sai dai a cewarsa, hatta kananan jiragen ruwan, ana biyan su ne da Dalar Amurka.