Dokar kayyade tsadar bukukuwan aure, zanen suna, kaciya da makamantansu a Sakkwato ta tsallake karatu na biyu a Majalisar Dokokin Jihar.
Wannan ya biyo bayan gabatar da kudurin dokar da Honarabul Abubakar Shehu Shamaki (APC- Yabo) ya gabatar tare da gudunmuwar Honarabul Faruku Balle (PDP- Gudu) a zaman Majalisar Dokokin a yau.
Da yake gabatar da dokar, Honarabul Shamaki, ya bayyana cewar dokar na da manufar kayyade da takaitawa daidai gwargwado kan tsada da sharholiya da ake yi a bukukuwan aure, zanen suna da kaciya a Sakkwato.
Ya ce ko shakka babu dabi’ar almubazzaranci da ake yi da sunan bukukuwa ba karamar illa ba ce wadda ke haifar da tabarbarewar tattalin arziki a cikin al’umma.
“Wannan bakar dabi’ar idan aka ci gaba a haka ba tare da daukar mataki da kayyadewa ba, za ta sa aure ya yi wa jama’a matukar wahala wanda hakan zai iya haifar da zina, madugo, luwadi da sauran ayyukan assha,” In ji shi.