Anyi wa kalamaina gurguwar fassara – Abdullahi Abbas

0
94

Shugaban jam’iyyar APC reshan jihar Kano, Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen da ake masa na amfani da kalaman tunzura gangamin yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa.

Kalmar “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai mun ci zaɓe”, ba baƙon abu ne domin an sha jiyo Abdullahi Abbas na ambato wadannan kalamai a tarukan siyasa tun daga zaben 2019.

Ƴan adawa a jihar na cewa irin wadannan kalamai na Abdullahi Abbas, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da babban zaɓe da ke tafe a jihar.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, shugaban APC a Kano ya ce an yi wa maganganunsa mummunar fahimta ce kawai.

A makon da ya gabata ne BBC ta kawo rahoto kan zargin da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na yin kalaman tunzura rikici.