Gwamnati ta dage dawo da jigilar jirgin kasan Abuja-Kaduna

0
103

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dage dawo da zirga-zirgar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da ta ayyana yi a yau ranar Litinin.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Ministan ya mayarwa da ’yan Najeriya murnarsu ciki a yayin rangadin da ya kai kan layin dogon da ke Kaduna domin tabbatar da matakin shirye-shiryen da aka kammala gabanin dawo da jigilar.

Ministan wanda bai fayyace ainhin ranar da za a dawo da jigilar ba, ya ce jinkirin da za a fuskanta ba zai wuce na tsawon mako guda ba.

A cewar ministan, “Gwamnatin Tarayya ta bullo da wani sabon tsarin siyan tikitin jirgin, wanda a cewarsa shi ne mafarin binciken tabbatar da tsaro wanda zai ba mu damar tantance wadanda ke hawa jirgin a kowane lokaci.”

A makon da muka yi bankwana da shi ne Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 28 ga watan Nuwamban 2022, a matsayin ranar da za a dawo da jigilar jirgin kasan da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja, babban birnin kasar.

An dai dakatar da sufurin jirgin ne a watan Maris din da ya gabata, bayan da ’yan ta’adda suka kai masa hari, inda suka kashe wasu fasinjojin suka kuma yi garkuwa da wasu.

Tsawon watanni da suka gabata ne dai aka dakatar da sufurin jirgin bayan da ’yan ta’adda suka dana abubuwan fashewa a kan layin dogo da jirgin ke zaraya a kansa.

’Yan ta’addan wadanda a yayin harin sun kashe fasinjoji 9, sun kuma sace fiye da fasinjoji 60, amma daga bisani duk sun kubuta.