Qatar 2022: Ghana ta sha da kyar a hannun Koriya ta Kudu

0
103

Kwallaye biyu da Mohammed Kudus ya jefa tare da guda da Mohammed Salisu ya zira a karawar da Ghana ta yi da Koriya ta Koriya sun taimaka mata samun nasara a ci gaba da wasannin cin kofin duniyar da ke gudana a kasar Qatar.

Wannan gagarumar nasarar ta farfado da damar da Ghana ke da ita ta zuwa zagaye na gaba, muddin kasar ta samu nasara a wasanta na karshe da za ta fafata da Uruguay.

Mohammed Salisu ya fara jefawa Ghana kwallo a wasan, yayin da Kudus ya jefa ta biyu a zagaye na farko.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Koriya ta Kudu ta farke ci biyun ta hannun dan wasanta Cho Gue-sung, abin da ya jefa fargaba tsakanin magoya bayan kasar Ghana.

A minti na 68 Mohammed Kudus ya jefa kwallo ta 3, abin da ya bai wa Ghana nasara, duk da yake ‘yan kasar Koriya ba su yi kasa a gwiwa ba, sakamakon munanan hare-haren da suka yi ta kai wa har zuwa lokacin tashi a wasan.