An roki A’isha Buhari da ta saki dalibin da ya ce ta yi ‘bulbul’

0
103

Iyayen dalibin nan na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Azare, sun roki uwargidan shugaban Najeriya, A’isha Buhari da ta yi wa Allah , ta yi hakuri ta bari a sake shi.

An dai kama dalibin ne wanda ke ajin karshe a jami’ar sakamakon rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana bayyana uwargidan shugaban kasar a matsayin wadda ta ci kudin talakawa ta yi bulbul tare da hada hotanta da rubutun.

Iyayen Aminu sun bukaci uwargidan shugaban kasar da ta yafe wa dalibin, suna masu cewa, ita uwa ce ga kowa.

A cewarsu, da farko ba su da masaniyar cewa an kama dansu, sai bayan kwanaki biyar suka samu labarin bacewarsa.

Iyayen sun ce, an tasa keyarsa zuwa birnin Abuja a ranar 17 ga wannan wata na Nuwamba, inda aka tsare shi tare da azabtar da shi a kan idon uwargidan shugaban kasar.