Makaman yakin Rasha da Ukraine na kwarara zuwa Tafkin Chadi – Buhari

0
104

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ana karkata wasu makaman da ake amfani da su a yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine zuwa Yankin Tafkin Chadi.

Buhari yace ya zama wajibi shugabannin dake yankin su tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace na dakile safarar kanana da manyan makaman dake kwarara zuwa yankin.

Shugaban yace babu tantama yakin Rasha da Ukraine tare da wasu tashe tashen hankulan dake ake fama da su a yankin Sahel sun taimaka wajen rura wutar rikicin Boko Haram a Tafkin Chadi.

Buhari yace duk da yake kasashen dake yankin sun yi kokari wajen dakile kaifin book haram da wasu kungiyoyi makamanta ta a yankin, har yanzu ana fuskantar barazanar yan ta’adda.

Shugaban wanda ya yaba da rawar da rundunar hadin kai ta kasashen guda 4 ke takawa wajen murkushe mayakan book haram, ya bukace sojojin da su kara kaimi wajen fadada nasarorin da suke samu na kawar da duk wata barazanar da kasashen yankin ke fuskanta.