A’isha Buhari ta yi wa Aminu afuwa

0
111

Uwargidan shugaban Najeriya’ A’isha Buhari ta janye karar da ta shigar a gaban kotu tana neman a hukunta dalibin nan da ya yi mata shagube, Aminu Mohammed bayan ta tasha matsin lamba daga Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama da kuma daidaikun jama’a.

Lauyan da ya shigar da karar, Fidelis Ogbobe ya bayyana cewa, uwargidan ta amince ta janye karar ne bayan wasu masu fada-a-ji a Najeriya sun tsoma baki cikin lamarin.

A yayin gabatar da hukuncinsa, alkalin babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja, Yusuf Halilu ya yaba wa A’isha Buhari kan matakin da ta dauka na yi wa dalilbin afuwa.

Alkalin ya kuma bukaci iyaye da su rika sanya ido kan ‘ya’yansu domin kaucewa sake aukuwar irin wannan al’amari.

Rahotanni sun ce, dalibin na jami’ar tarayya da ke Jigawa, ya sha duka a hannun wasu jami’an tsaro kafin a gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin sa da fadin wasu kalamai ga uwargidan shugaban kasar.