Sojoji sun cafke ‘yan bindiga 5, sun kwato N20m a Katsina

0
103

Dakarun ‘Operation Hadarin Daji’ sun kama wasu ’yan bindiga biyar a kauyen Daudawa da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina tare da kudi Naira miliyan 19.5 a hannunsu.

Daraktan Yada Labarai rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka ne a taron mako biyu kan ayyukan sojoji a fadin Najeriya a ranar Alhamis a Abuja.

Danmadami, ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri, ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022.

Ya kuma kara da cewa sojojin sun kwato wata mota da wayoyin hannu guda biyar daga hannun wadanda ake zargin.

Ya ce sojojin sun kuma kashe ‘yan bindiga uku a kauyen Yambuki da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022 yayin da wasu suka gudu da raunuka.

Danmadami, ya ce sojojin sun kwato manyan bindigogi guda 91, bindig kirar AK-47 guda 2 da kuma babura guda uku.

Ya ce sun kuma kama wani da ake zargin dan bindiga ne dauke da harsashi 269 a hanya Zariya zuwa kauyen Damari a Karamar Hukumar Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.

“Saboda haka, a tsakanin ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2022 sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda takwas, alburusai 91 da kuma bindigogi kirar gida guda biyar.

 

AMINIYA