Ɗalibin jami’ar UNIBEN ya ƙera mota ƴar-ƙurƙura

0
92

Wani dalibin digiri na uku, daga tsangayar ilimin Injiniyanci a Jami’ar Benin, mai suna Igbinosa Eghosa, ya kera mota samfurin ƴar-ƙurƙura.

Eghosa na Sashen ilimin ƙere-ƙere, ya kirkiro motar a karkashin kulawar Farfesa Akaehomen Ibhadode, wanda kuma ya jagoranci tawagar wajen gabatar da motar ga shugabannin Jami’ar.

A cikin wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a shafinta na Facebook na UN a jiya, Alhamis, wanda ya ƙirƙiri motar ya ce za ta taimaka wajen habbaka harkar sufuri da noma a Nijeriya.

Ya kara da cewa idan aka samu isassun kudade, za a iya kera motar da yawa saboda tsarin na iya magance bukatun sufuri ko da a cikin al’ummomin yankin.

A nasa bangaren, mai kula da aikin da ɗalibin ya yi, ya nuna cewa sama da kashi 80 cikin 100 na kayayyakin da ake amfani da su wajen kera motar ana samun su ne a cikin gida Nijeriya.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Lilian Salami, ya yaba wa waɗanda su ka saka hannu a aikin ƙera motar, don inganta ayyukan gida tare da bayyana shirye-shiryen Jami’ar don haɗin gwiwa tare da tsangayar domin ƙera wa jami’ar motoci domin ta yi amfani da su.