Almundahana: Buhari ya kori shugaban hukumar NIRSAL

0
92

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban Hukumar Bada Lamunin Noma, NIRSAL, Aliyu Abdulhameed daga mukaminsa sakamakon zargin sa da cin hanci da rashawa.

A cikin watan Janairu da ya gabata, Jaridar Daily Trust ta gudanar da bincike kan yadda hukumar ta hada baki da wasu kamfanoni wajen karkatar da wasu biliyoyin kudi da aka ware domin girbe kadada dubu 20 na alkama a jihohin Kano da Jigawa.

Abdullhameed ya musanta wannan zargin, yana mai cewa, wasu mutane ne suka shirya masa gadar-zare domin zubar masa da kimarsa da ta hukumarsa.

Bayan rahotron na Daily Trust, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta gayyaci Abdulhameed da wasu jami’ansa domin amsa tambayoyi kan zargin almundahanar.

Kazalika jami’an ‘yan sanda su ma sun gudanar da bincike a kansa.