Buhari ne ya jefa ‘yan Najeriya cikin kangin talauci – Gwamnoni

0
122

Gwamnonin Najeriya 36 sun shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewar gazawarsa wajen samar da tsaro da kuma kasa cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya ne dalilan da suka jefa jama’ar kasar nan cikin halin kunci rayuwa da talauci.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnonin, Abdurazaque Bello-Barkindo, ya rabawa manema labarai, ta ce abin takaici ne yaddda gwamnatin tarayya ke neman dora wa gwamnonin laifi dangane da irin talauci da halin kuncin da mazauna yankunan karkarar kasar nan ke fama da su.

Gwamnonin sun ce a 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewar zai fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talaucin da ya addabi jama’a, amma a yau alkaluma sun nuna cewar ‘yan Najeriya sama da miliyan 130 ne ke fama da talauci, inda suke rayuwa kasa da Dala guda a kowace rana.

Sanarwar ta ce a karkashin gwamnatin Buhari, an kwashe watanni kamfanin man NNPC ba ya iya zuba ribar da yake samu a asusun gwamnati, abin da ya tilasta wa gwamnonin neman mafita ta wasu hanyoyi wajen samun kudaden shiga domin cike gibin kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya domin sauke nauyin da ke kansu a bangare noma da raya karkara da ayyukan jinkai da kuma kula da lafiyar jama’a.

Gwamnonin sun kuma caccaki ministan kasafin kudi, Clement Agba, wanda ya zargi gwamnonin da jefa mutane sama da kashi 72 a yankunan karkara cikin talauci da shara karya wajen kauda kan jama’a daga assalin abin da yake faruwa.