Likitoci 10,000 kacal ne suka rage a Najeriya – NARD

0
107

Kungiyar likitocin Nijeriya (NARD) ta bayyana cewa yawan likitocin kasar nan suna raguwa a kullun, inda ta ce a halin yanzu likitoci 10,000 kacal ne suka rage.

Shugaban kungiyar NARD, Dakta Emeka Orji shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata.

A cewar Orji, sama da likitoci 100 suke barin kasar a duk wata wajen neman aiki mai gwabi a kasashen ketare.

Ya ce, “Na sani a halin yanzu muna da likitoci 24,000 ciki har da kwararu da likitocin gida da sauran ma’aikatan lafiya. A cikin likitoci 80,000 da aka yi wa rajista, kashi 64 ba sa gudanar da aikin, wasu sun fice daga kasar, yayin da wasu sun yi ritaya, wasu sun sauya aiki, wasu kuma sun mutu.

“Likitocin gida da muke amfani da su guda 16,000 a baya, amma a yanzu muna da 9,000 zuwa 10,000. Ba za mu iya tantance yawan likitocin ba a kullum, saboda ficewa da suke yi. Saboda haka, a yanzu haka muna da likitoci a tsakanin 9,000 zuwa 10,000 a fadin kasar nan.