Gamayyar shugabannin Kiristoci da jagororin siyasa Musulmai da ga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya, FCT, sun amince da mara wa dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar baya a zaben 2023.
Bayan taron shugabanni da wakilai da ga sassan arewacin kasar da su ka hada da shugabannin addinai da kungiyoyin mata da matasa, sun dauki matakin ne a Abuja jiya Jumaâa a dakin taro na Atiku Abubakar da ke cibiyar Shehu Musa Yaradua.
Taron ya amince da rahoton kwamitin kwararru na IRS, karkashin jagorancin tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Mohammed Kumalia da Nunge Mele, SAN.
Idan dai ba a manta ba a ranar 8 ga watan Oktoba ne kungiyar shugabannin addinin kirista da musulmin Arewa ta kafa kwamitin da zai ba da shawarar tsarin da Najeriya ta dauka a zaben shugaban kasa na 2023.
Kudurin na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto kuma ministan albarkatun ruwa a zamanin gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo, Mukhari Shagari da D.D.Sheni su ka sanya wa hannu.