Sojoji sun ragargaza ‘yan bindiga mukarraban Alhaji Leyi, sun ceto mutum 5

0
139

Jami’an rundunar hadin guiwa ta tsaro sun halaka ‘yan bindiga 20 tare da ceto wasu mutum 5 da aka yi garkuwa dasu yayin samamen da suka kai Gaskiya Bana, kauye mai iyaka da jihohin Niger da Kaduna a karamar hukumar Munya ta jihar Niger, jaridar The Nation ta ruwaito.

Wadanda aka yi garkuwa dasu din an gano sun kwashe wata daya a hannun ‘yan bindigan.

‘Yan bindigan an gano suna aiki ne da rikakken shugaban masu garkuwa da mutane, Alhaji Leyi, wanda ya kafa dabarsa kuma yake barna a Gaskiya Bana dake karamar hukumar Munya.

Aiki da dakarun suka yi ya kwashe sa’o’i biyar.