‘Yan bindiga sun sace mamu, da mutane 18 a masallaci a Katsina

0
92

‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace masallata kusan 20 a wani masallaci a ƙauyen Maigamji da ke yankin ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina.

Rahotonnin sun ce maharan sun kai farmaki masallacin ne ranar Asabar da daddare lokacin da masallatan suka taru domin gudanar da sallar Isha’i.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar katsina SP Gambo Isah ya shaida wa BBC cewa an raunata limamin masallacin tare da wani mutum guda, an kuma sallamo su daga asibiti bayan yi masu magani.

SP Gambo ya ce tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi sojoji da ‘yan sanda da ‘yan sa kai sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sacen.

To amma ya ce har yanzu ba a ga mutum 13 ba. Ya kuma ƙara da cewa jami’an tsaro na bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun kuɓutar sauran mutanen da suka rage a hannun maharan.

Harin dai shi ne na baya-bayan nan, yayin da ƙasar ke fama da yawaitar hare-haren masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Jihar Katsina – wadda ita ce mahaifar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari – na cikin jihohin ƙasar da ke fama da tashe-tashen hankula masu alaƙa da ayyukan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Matsalar rashin tsaro dai ta kasance wani babban al’amari da jam’iyyun siyasa a ƙasar ke sanyawa cikin manyan manufofin yaƙin neman zaɓensu, yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓe a farkon shekara mai kamawa.