An fara aiki da farashin da aka kayyade wa danyen man Rasha

0
91

A Litinin din aka fara amfani da farashin danyen man Rasha, wanda tarayyar Turai, kungiyar G7 da Australia suka kayyade, a kokarin da suke na takaita kudin shiga ga Rashar, tare da tabbatar da cewa ala tilas ta ci gaba da samar da makamashi ga kasuwannin duniya.

Kayyadadden farashin ya soma aiki ne tare da takunkumin da Tarayyar Turai ta kakaba wa Rashar a kan danyen man da take fitarwa ta ruwa, wanda ke zuwa watanni da dama bayan wadda Amurka da Canada suka antaya mata.

Rasha ce kasa ta biyu a cikin masu  fitar da danyen mai a duniya, kuma idan ba a kayyade farashi ba, za ta samu sabbin abokan hulda cikin sauki.

Wannan mataki na nufin cewa, danyen man da za a sayar a kan farashin dala 60 ko kasa da haka ne kawai Rasha za ta iya fitarwa, kuma za a haramta wa kamfanonin da ke Tarayyar Turai da G7 bai wa jirgin dakon man da ya zarta wannan farashi inshora.

Kwararru dai sun bayyana fargaba a kan abin da ke je ya zo a game da wannan kayadden farashi a kasuwannin danyen mai, musamman martanin kungiyar OPEC.

Amma Tarayyar Turai ta zake cewa sai taimaka wajen samar da daidaito a kasuwannin, kuma kai tsaye  kasashe masu tasowa za su fa’idantu da matakin, wanda zai sa a rika samun danyen man Rasha a farashi mai rahusa.

Sai dai a martanin da ta mayar ta wata sanarwa daga fadar shugaban kasar, Rasha ta ce matakin da aka dauka a kanta ba zai dankwafe karfinta a yakin da take da Ukraine ba.