An kona ofishin gwamna kan tsadar rayuwa a Syria

0
104

An kashe mutum biyu, a yayin da masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa suka kai hari tare da kona ofishin gwamna bayan arangama da jamiā€™an tsaro a birnin Sweida da ke Kudancin kasar Syria.

Daruruwan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Syria sun yi dafifi a ofishin gwamnan da ke birnin Druze, suna wake-waken neman kawar da mulkin Shugaba Bashar Assad, saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki, kafin su kutsa cikin ginin a ranar Lahadi.

Wani dan gwagwarmaya kuma editan kafar Suwayda 24, Rayan Maarouf, ya ce, ā€œAn kona ofishin gwamnan gaba daya ta ciki,ā€ kuma an raunata mutane da dama a yayin musayar wuta.

Rayan Maarouf ya ce, ā€œAn bude wuta babu kakkautawa,ā€ amma babu tabbacin ko ā€™yan sandan da ke wurin ne suka bude wuta.

Kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ce masu zanga-zangar da suka shiga ofishin sun kona muhimman takardu ā€” duk kuwa da cewa gwamnatin Syria ba ta lamuntar zanga-zanga a yankunan da ke karkashin ikonta.

Maā€™aikatar Harkokin Cikin Gida ta Syria ta ce masu boren sun yi kokarin kwace hedikwatar ā€™yan sanda da ke birnin, inda aka kashe wani dan sanda a arangamar.

Sanarwar da ta fitar ta ce, ā€œZa mu bi sahun bata-garin da suka nemi kawo barazanar tsaro a birnin domin su fuskanci hukunci.ā€

Wasu shaidu sun ce gwamnan ba ya ofishin a lokacin da aka kai mamayar aka lalata ofishin.

Wani shaida ya ce wani farar hula da aka kai asibiti bayan samun raunin harbi, ya rasu, wani kuma na samun kulawa daga raunin harbin da ya samu.

Lardin Sweida na daga cikin yankunan da ba su shiga tashin hankalin da ya biyo bayan boren neman kawar da gwamnatin Shugaba Assad a guguwar neman sauyi a kasashen Laraba da ta taso sama da shekara 10 da suka wuce ba.

Yawancin alā€™ummar yankin Druze, wadanda Musulmi ne, sun kaurace wa rikicin kasar, duk da cewa wasu daga cikin shugabannin addini a yankin ba su goyon bayan masu son shiga aikin sojin kasar.

Syria na fama da matsin rayuwa, tun bayan barkewar rikicin da ya yi ajalin dubban daruruwan mutanen kasar tare da mayar da wasu milioyi ā€™yan gudun hijira.