An sake ƙona ofishin INEC a Imo

0
83

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa wasu ɓatagari sun sake ƙona ofishinta da ke karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar Imo.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a yau Lahadi a wata sanarwa.

A cewarsa, kwamishinan zabe na jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu ce ta bada rahoton cewa an kai hari kan ofishin hukumar dake karamar hukumar Oru ta yamma da misalin karfe 4.00 na safiyar yau Lahadi.

“Harin ya shafi dakin taro ne inda aka lalata kayayyakin ofis da kayan aiki. Sai dai kuma harin bai shafi sauran wurare masu mahimmanci ba, ”in ji Okoye.

Ya kuma tuna cewa ko a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, 2022 an kai hari ofishin INEC a karamar hukumar Orlu ta jihar Imo.

Ya ce, “Gaba daya, wannan shi ne hari na 7 da aka kai wa cibiyoyinmu a jihohi biyar na tarayyar kasar nan cikin watanni hudu da su ka gabata.

Har wa yau, hukumar ta na mai bayyana damuwarta kan sakamakon hare-hare da ake kai wa cibiyoyinta a fadin kasar nan zai kawai naƙasu a kan gudanar da zabe mai zuwa,