Iran ta soke rundunar ‘yan sandan tabbatar da da’a ta kasar

0
91

Gwamnatin Iran ta sanar da soke bangaren jami’an ‘yan sandan tabbatar da da’a a kasar, bayan zanga zangar da aka shafe kusan watanni 3 ana yi kan mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka zarga da keta dokkokin addini.

Zanga zangar da mata suka jagoranta a Iran, wadda hukumomi suka kira tarzoma ta yi sanadiyar dankwafar da al’amura a kasar, tun bayan da Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 a duniya, ta gamu da ajalinta a ranar 16 ga watan Satumban da ya gabata, kwanaki 3 bayan jami’an ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a suka tsare ta.

Masu zanga zangar  sun kona hijabansu inda suke rera wakokin sukar gwamnati, abin da ya sa da dama daga cikin su suka daina amfani da hijabi musamman a wasu sassa na birnin Tehran

Kamfanin dillancin labaran Iran ISNA ya ruwaito Ministan shari’ar Kasar Mohammad Jafar Montazeri yana cewa rundunar ‘yan sandan tabbatar da ‘da’a basu da damar zartar da hukunci a kan kowanene, saboda haka an soke su.

Kalaman Montazeri na zuwa ne a wani taron addini da aka gudanar, inda yake amsa tambayoyi a kan dalilin soke rundunar baki daya.

Zanga zangar dai ita ce irinta na farko cikin shekaru da dama a  kasar,, wadda tayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 300, cikin su har da jami’an tsaro.