Yadda aka sace mutum 46 a jihar Katsina

0
109

’Yan bindiga sun nemi a biya su kudin fansa da sabbin takardun Naira bayan sun yi garkuwa da mutum 46 a wasu hare-hare biyu a kauyukan kananan hukumomin Funtua da Batsari na jihar Katsina.

Mahara kusan 40 a kan babura, sun kashe mutum daya, suka sace wasu 28, ciki har da  mata da kananan yara a safiyar ranar Juma’a, a kauyen Karare da ke Karamar hukumar Batsari.

“Daga cikin mutum 28 da suka sace har da wasu dalibai,” in ji wani ganau da ya ce maharan sun kashe mutum daya a yayin da suka shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

Rahotanni sun nuna daga cikin yaran da aka yi garkuwa da su har da dalibai daga kauyen Kokiya da ke hanyarsu ta zuwa Makarantar Sakandaren Je-ka-ka-dawo ta Gwamnati a kauyen Karare.

Shaidan ya ce, “Daga baya maharan sun sako mutum hudu daga cikin wadan da aka sace, wato Malam Ladan da ’ya’yansa uku.