‘Yan bindiga a jamhuriyar Nijar, na ci gaba da amsa kiran hukumomin ƙasar ta hanyar ajiye makamai, inda suke fitowa suna rungumar shirin zaman lafiya.
‘Yan bindigar tamanin da shida ne suka mika wuya ciki har da mace guda.
‘Yan bindigar sun ce sun amsa kiran da shugaban kasar Muhammed Bazoum, ya yi musu ne a kan su ajiye makamai tare da kawo karshen miyagun dabi’un da suka runguma.
Wadanda suka mika wuyar sun ce rashin aikin yi ne ya sa suka shiga cikin ayyukan ta’addanci.
Daya daga cikin ‘yan bindigar da ya ajiye makami ya shaida wa manema labarai cewa, baya ga sayar da makamai har satar mutane, kai hare-hare garuruwa daban-daban da ma kisa duk ya yi.
Ya ce amma yanzu duk ya tuba ya daina, kuma yana godewa wadanda suka já hankalinsu a kan su bari, sannan ya yi kira ga matasa a kan su daina aikata duk wasu abubuwa da suka san basu da kyau.
Ita ma mace daya tilo daga cikin mutum 86 da suka tuba daga aikata ta’addancin ta shaida wa BBC cewa, ita sana’arta ita ce saukar ‘yan bindigar suna ba ta kudi.
Ta ce “Duk na san sana’ar da suke hakan bai hanani basu masauki ba idan sun zo domin suna ba ni kudi, to amma a yanzu na duba na daina duk barazanar da suke mini.”
Ministan cikin gidan jamhuriyar ta Nijar, Hammadou Adamu Sule, ya shaida wa BBC irin kokarin da shugaban kasar ya yi wajen jan hankalin ‘yan bindigar a kan su ajiye makaman.
Ya ce suna fatan da sannu a hankali sauran ‘yan bindigar ma zasu ajiye makamai.
‘Yan bindigar da suka mika wuyan sun bukaci shugaba Muhammed Bazoum, a kan ya samar musu da ayyukan yin da za su ba su damar bawa wadannan miyagun dabi’un da suka bari baya har abada.
Suka ce suma suna so su zama ‘yan kasa na gari wadanda al’ummarsu zata yi alfahari dasu.
A garin Bangui, ɗaya daga cikin yankunan kasar masu fama da hare-hare, gwamnatin ƙasar ta kafa sansani inda take tsugunnar da irin waɗannan tubabbun mayaƙa don gyara musu hali da horas da su sana’o’in dogaro da kai.