Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Najeriya, bayyana cewa har yanzu ba a shawo kan matsalar jin kai a yankin Arewa maso Gabas ba, yayin da mata da kananan yara suka rasa muhallan su a shekarar 2022.
A cewar rahoton majalisar dinkin Duniya a cikin 2023, miliyoyin mutane a Njjeriya za su ci gaba da fuskantar talauci, yayin da da dama kuma za su yi ta fadi tashin neman abinci.
Arewa maso gabashin Nijeriya ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya, inda akalla mutane sama da miliyan takwas ke bukatar agaji a shekarar 2023.
Matsalolin da mata da maza da yara ke fama da su a kowace rana a fadin Jihohin Borno da Adamawa da Yobe har yanzu na karuwa, a cewar rahoton.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar kusan Dala biliyan 1.2 domin tallafawa mutane miliyan 5.4 a fadin Najeriya.
Rahoton ya kara da cewa bukatun jin kai sun karu matuka saboda yakin da ake yi a Kasar Ukraine da kuma tasirin matsalar sauyin yanayi a yankin gabashin Afirka da yankin Sahel da Pakistan da kuma Najeriya.
“A yankin Yamma da Tsakiyar Afirka kadai, ana sa ran mutane miliyan 69 za su bukaci agajin jin kai a shekarar 2023, inda ake fargabar cewa Arewa maso gabashin Najeriya da Burkina Faso, wadanda ke fama da matsananciyar yunwa, za su iya shiga cikin mummunan yanayi, musamman idan matsalar sauyin yanayi ta tsananta,” in ji Majalisar Dinkin Duniya.
Rahoton ya ci gaba da cewa, a shekarar 2023, mutane miliyan 339 a fadin duniya za su bukaci agajin jin kai, wanda ya karu da kusan kashi 24 cikin dari idan aka kwatanta da bara.
Rahoton ya kara da cewa bukatun jin kai sun karu matuka saboda yakin da ake yi a Kasar Ukraine da kuma tasirin matsalar sauyin yanayi a yankin Gabashin Afirka da yankin Sahel da Pakistan da kuma Nijeriya.
“A yankin yamma da tsakiyar Afirka kadai, ana sa ran mutane miliyan 69 za su bukaci agajin jin kai a shekarar 2023, inda ake fargabar cewa Arewa maso Gabashin Nijeriya da Burkina Faso, wadanda ke fama da matsananciyar yunwa, za su iya shiga cikin mummunan yanayi, musamman idan matsalar sauyin yanayi ta tsananta,” in ji Majalisar Dinkin Duniya.