Abin da ‘yan Najeriya ke cewa kan matakin CBN na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa kullum

0
280

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu game da sabon matakin da babban bankin ƙasar CBN ya ɗauka na taƙaita yawan kuɗin da za a iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki.

A ranar Talata ne dai babban bankin Najeriya CBN ya fitar da sababbin dokoki na hada-hadar kuɗaɗe a bankunan ƙasar.

A cikin sabbin dokokin, CBN ya ce daga ranar tara ga watan gobe yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

Haka kuma CBN ɗin ya ce yawan kuɗin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cirar kuɗi ta ATM a sati shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a rana naira 20,000 ne kacal a na’uran ATM da kuma wajen masu amfani da POS.

Tun bayan fitar da sabbin dokokin ‘yan ƙasar ke tofa albarkacin bakinsu, a yayin da wasu ke sukar matakin wasu kuma cewa suka yi suna maraba da matakin.