Miliyoyin ‘yan Najeriya za su fuskanci yunwa a 2023 – FAO

0
121

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO tace ‘Yan Najeriya kusan miliyan 25 da rabi ne zasu fuskanci matsalar karancin abinci tsakanin watan Yuni zuwa Augustan shekara mai zuwa, kamar yadda binciken da ta gudanar ya tabbatar mata.

FAO ta gargadi gwamnatin Najeriya cewar muddin ta kasa daukar matakan da suka dace domin magance wannan hasashe, matsalar na iya shafar karin mutane miliyan 4 da kusan rabi dake jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.

Rahotan da kungiyar ta fitar, yace a watan Oktobar da ta gabata, ‘yan Najeriya miliyan 17 ke fama da wannan matsala ta karancin abinci, cikinsu harda ‘yan gudun hijira dake jihohi 26 tare da Abuja da kuma wasu miliyan 3 dake jihohin Borno da Adamawa da Yobe.

Domin kai dauki ga irin wadannan mutane, gwamnatin kasar Norway ta sabunta tallafin kudaden da take baiwa Hukumar FAO domin taimakawa irin wadannan mutane a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da kuma Taraba.

Ana saran tallafin na Norway ya kaiga akalla gidaje kusan dubu 44, mai dauke da mutane sama da dubu 300, kuma akalla kashi 45 na mutanen da zasu ci gajiyarsa mata ne wadanda zasu karbi tallafin kayan noma da kiwo da na’urar girkin da baya gurbata muhalli da kuma wasu kayayyaki.

Jakadan Norway a Najeriya Knut Eiliv Lein yace kasarsa a shirye take ta ci gaba da taimakawa mutanen da tashin hankalin arewa maso gabashin Najeriya ya tagayyara.