Davido zai yi wasa a bikin rufe gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar

0
196

Mawakin Najeriya, Davido na shirin yin waka a bikin rufe gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar,da an kasuwan Hong Kong, Stephen Hung ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis ta shafinsa na Instagram.

Ya yi ikirarin cewa Davido ya bayyana a hukumance cewa zai rufe bikin gasar cin kofin duniya, da yake nuna farin ciki, Stephen Hung ya bayyana cewa ba zai iya jira ya gan shi ba.

“Na yi matukar farin ciki da dan uwana @davido ya tabbatar da cewa zai taka rawar gani a bikin rufe gasar cin kofin duniya na Qatar.”

“Ba zan iya jira in gan shi a can ba,” ya rubuta.

A cewar majiyoyi, Davido zai yi wakar gasar cin kofin duniya ta Qatar “Hayya Hayya (Happy Together)” tare da mawakiyar Trinidadiya Cardona da kuma mawakiyar Qatar Aisha a yayin bikin rufe gasar da aka shirya yi ranar Lahadi.