Sojojin Najeriya sun musanta zargin zubar wa mata ciki a Borno

0
88

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta mayar da martani kan rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya zargi sojojin ƙasar da aiwatar da wani shirin zubar wa matan da mayaƙan Boko Haram suka yi wa fyaɗe ciki.

Shalkwatar tsaron ta bayyana rahoton na Reuters a matsayin labarin kanzon kurege.

Tare da cewa wani shiri ne na shafa wa sojojin Najeriyar kashin kaji.

Shugaban sashen yaɗa labaru na shalkwatar tsaron Manjo Janaral Jimmy Akpor ya ce tun daga watan Yulin 2021 har zuwa watan Nuwamban bana mayaƙan Boko Haram sama da dubu 82 tare da iyalansu ne suka yi saranda ga dakarun ƙasar kuma fiye da dubu arba’in daga ciki yara ne.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno ta samar wa tsoffin mayaƙan Boko Haram da iyalan nasu matsugunai domin ba ta son ta raba yaran da iyayensu.

Shalkwatar tsaron ta kuma ƙara da cewa an haifi jarirai 262 a cikin wannan sansani, cikin watanni huɗu.

Rahoton na kamfanin dillancin labaru na Reuters ya yi zargin cewa an tilasta wa mata da yara mata dubu 12 zubar da ciki tun daga 2013 karkashin wani shiri da aka aiwatar cikin sirri.