Wahalar man jirgi: Air Peace ya sanar da yiwuwar samun jinkirin tashin jirage

0
87

Mahukunta a Kamfanin Zirga-zirgar jiragen sama na Air Peace sun sanar da yiwuwar samun jinkirin na tashin jirgen sakamakon wahalar man jirgi, wanda aka fi sani da Jet A1.

Kamfanin jirgin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta kafar sadarwar Instagram da jaridar Punch ta samu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “ A sa ran samun tsaiko a Jigilar jiragenmu yayin da mu ke fama da karancin man jirgi wanda ke jawo mana tsaiko.

“Mu na fatan lamarin zai dawo daidai nan ba da jimawa ba. Mun yi nadamar tasirin wannan a kan tsare-tsaren ku.