Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari asibitin Anambra sun sace jarirai 4

0
106

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani asibitin haihuwa da ke Nkpologwu, karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra, inda suka yi awon gaba da jarirai hudu.

Vanguard ta tattaro daga wata majiya a unguwar cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, kuma sai da al’ummar yankin suka sanar da su a safiyar Laraba.

A cewar majiyar, “Al’amarin ya faru ne a unguwar mu, kuma tun da safiyar Laraba mutane suke ta tattaunawa.

“Sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki asibitin (an sakaya sunan su) suka tafi da jarirai hudu daga asibitin. Jarirai sabbin haihuwa.