DSS ta bai wa NNPC da sauran su wa’adi na kawo karshen matsalar mai a Najeriya

0
88

Hukumar Tsaron Farin kaya ta Najeriya DSS ta bai wa kamfanin mai na kasar wato NNPC da kungyar dillalan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin sa’o’i 48 su kawo karshen karanccin man fetur da ya addabi al’umma.

Hukumar DSS din ta yi barazanar cewa za ta kaddamar da samame da zarar wa’adin da ta diba ya cika, kuma dogayen layuka ba su gushe a gidajen mai ba.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ne ya shaida wa manema labarai haka a wai jawabi da ya yi musu jim kadan bayan shugaban hukumar Yusuf Bichi ya gana da masu ruwa da tsaki a bangaren mai.

Hakan na zuwa ne sakamakon dogayen layuka da ake samu a gidajen mai na sassan kasar ciki harda abuja babban birnin Najeriyar da Lagos cibiyar kasuwanci.