Babu layuka a gidajen mai na Abuja bayan wa’adin DSS

0
95

Hukumar tsaro ta farin kaya,DSS, ta baiwa ‘yan kasuwa wa’adin sa’o’i 48 don kawo karshen matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin Najeriya, a gidajen man da ke Abuja da wasu yankuna yanzu kam su ragu.

Binciken da aka yi a birnin na Abuja ya nuna cewa har yanzu an rufe akasarin kasuwanin bayan fage inda ‘yan kasuwar  ke sayar da man a kan Naira 300 kan kowace lita, sabanin Naira 350 da ake sayar da su a kwanakin baya.

Binciken ya kuma nuna cewa galibin tashoshin da ke kan hanyar Kubwa da suka hada da Shema, Salbas, NIPCO, Eterna suna da gajerun layuka ba kamar kwanaki ba kafin hukumar DSS ta baiwa ‘yan kasuwa wa’adin sa’o’i 48 don samar da man ga jama’a.

Sai dai lamarin ya sha bamban a gidan mai na Eterna da ke kan hanyar Kubwa dab da Expressway yayin da tashar ta kasance a rufe ga jama’a a wani lokaci da aka hango ma’aikatan gidajen mai suna tururuwa suna jiran umarni.

A gundumar Utako da ke cikin birnin Abuja, an kuma rufe galibin gidajen mai.