Kofin duniya: Morocco ta kafa sabon tarihi a Afrika yayin da ta doke Portugal

0
100

Kungiyar Atlas Lions ta Morocco ta samu tikitin shiga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar, bayan da ta doke Portugal da ci 1.

Nasarar ta sa kasar ta zama tawaga ta farko a nahiyar Afirka da ta kai wannan mataki a gasar cikin shekaru 92 da ta yi.

Youssef En-Nesyri ne ya farke kwallon a minti na 42 da fara wasa kuma kungiyar ta Afirka ta ci gaba da ganin wasan.

An kori Walid Cheddira ne saboda cin zarafi da ya yi a karo na biyu amma hakan bai hana tawagar Arewacin Afirka ci gaba da kafa tarihi ba.

Morocco ta doke Spain a zagaye na 16 na karshe bisa hasashen masu sharhi.

 

.