Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin mu, lauyan Nnamdi Kanu Ejimakor ya koka

0
81

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), mai baiwa Nnamdi Kanu shawara na musamman, Aloy Ejimakor ya koka kan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai a mahaifarsa ta Urulla, karamar hukumar Ideato ta Arewa a jihar Imo a ranar Juma’a.

Ejimakor ya bayyana haka ne ga jaridar Vanguard da safiyar ranar Asabar tare da wani hoton bidiyo da ke nuna yadda wata kasuwa ta kone kurmus inda ya kara da cewa ‘yan bindigar sun far wa ‘yan uwansa tare da lalata musu kadarori.

A cikin sakon, Ejimakor ya ce shi da mutanen sun yi Allah wadai da harin na dabbanci kuma sun ji takaicin lamarin.

Lauyan shugaban kungiyar IPOB ya ci gaba da cewa lamarin zai ci gaba da wanzuwa cikin mutunci.

Ya ce, “A yau (Juma’a) 9 ga Disamba 2022, wasu ‘yan bindiga da dama sun mamaye garinmu, suka far wa ‘yan uwana, suka lalata musu dukiya tare da kona babbar kasuwarmu, mintuna biyar da gidana.

“Rana ce da za ta kasance har abada cikin rashin kunya. Na damu sosai; mutanena sun damu matuka.”

Da aka tambaye shi game da wadanda suka kai harin, Ejimakor ya ce bai san wani bayani ba game da maharan da suka kai harin.