Yadda ‘yan kasuwa ke asara kan tashin farashi

0
110

Biyo bayan tashin gwauron zabin kayan masarufi a kasar nan, shi ya janyo kananan masu sayar da kayan, tabka asara saboda samun raguwar abokan cinikayya.

Wata mata mai sayar da doya a kasuwar Karmo a babban birnin tarayyar Abuja uwargida Rukayyah Muhammed ta sanar da cewa, ci gaba da samun hauhawan farashin kaya a kasar nan, ya janyo wasu abokan cinikayyar ba sa iya sayen kayan na masarufi saboda samun raguwar kudaden shigar su.

Rukayyah Muhammed ta ce, farashin Doya guda 100, ya kai daga naira 40,000 zuwa naira 50,000, inda ta ce, wamnan ya danganta da irin girman da Doyar Leda shi.
A cewarsa, a baya ta na sayar da doyar da yawanta ya kai guda 300, amma saboda sautin farashin, a yanzu ina shan wuya wajen sayar da guda 200.

Ta ci gaba da cewa, a yanzu yawan irin wannan adadin na doyar, ana sayar wa daga naira 80,000 zuwa naira 100,000 ko kuma sama da hakan, inda ta kara da cewa, abokan cinikayyata, na yin korafi a kan farashin saboda ba su da isassun kudin da za su saya.

Shi ma wani karamin dan kasuwa mai sana’ar sayar da Fawa mai suna Awalu Abdulrahim Abdullahi ya sanar da cewa, a baya, farshin buhun dawa daya, ya kai daga naira 10,000 zuwa naira15,000
Abdullahi ya ci gaba da cewa, saboda kalubalen rashin tsaro a kasar nan, a yanzu farashin Kwaurar Dawa buhu daya mai nauyin kilo 90, ya kai naira 32,000
32,000, inda ya yi nuni da cewa, hakan na shafar sana’ar ta mu.

A cewar Abdullahi, jama’a a yanzu ba sa sayen kaya na kamar a baya, inda ya ce, idan abokin cinikayya na da burin sayen misali mudu biyar, ba fi ya iya sayen mudu biyu ko uku ba, saboda tashin farashin na dawa.

Ya ce, yana biyan daga naira 300 zuwa naira 500 na jigilar kowanne buhu daya daga jihar Neja ko zuwa kaduna amma a yanzu saboda tsadar man dizil da man fetur yana biyan naira 1000 ne a jigilar kowanne buhu daya.

Shi ma a na sa bangaren Salisu Abubakar ya ce, a baya yana sayen buhu daya mai nauyin kilo 50 akan naira 15,000, amma a yanzu, yana sayen sa akan naira 38,000, inda ya kara da cewa, shinkafa samfarin Gerawa Premium wacce ake sayar da buhunta daya daga naira 13,000 zuwa naira 14,000 a yanzu ana sayar da ahi akan naira 34,000.

Har ila yau, wannan ya kuma janyo rashin samun riba mai yawa da rashin sayar da kayan da yawa, inda ya ce a baya yana sayen buhu uku na shinkafar akan farashin naira 1000, amma a yanzu, bai fi kudin su saya masa buhuk biyu na shinkafar ba.

Wannan lamarin ya janyo wa mutane karfinsu na sayen kayan masarufin, tare da karya masu kwarin gwiwar sayen kayan may yawa.

A bisa binciken da aka gudanar a kasuwar yaa nuna cewa, farashin mudu daya na shinkafar da ake noma wa a cikin kasar nan, ya kai daga naira 1,200 zuwa naira 1,800
Buhu daya kuma na wake wanda a baya ake sayar da shi akan naira
32,000 a yanzu, ana sayar da shi akan naira 58,000.

Bugu da kari, jarka daya man gyada cin lita 25 ana sayar da ita akan naira 50.
Alhaji Abubakar ya ce, wannan shi ne, babban dalilin da ya sa akasarin shagunan ke fuskantar karancin tarwada, inda ya ce, a yanzu ana sayar wa a kan naira 160,000 sabanin yadda ake sayar wa a baya a kan naira 90,000.