‘Yan bindiga sun kashe mutane 3, sun kone gidaje 22 a Gombe

0
102

Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane uku tare da kone gidaje 22 a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Billiri a Jihar Gombe da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Adamu Kubto Dishi ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Gombe.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun harbe mutane biyu a kauyen Pobawure da wani mutum a kauyen Amtawalam tare da cinnawa gidaje wuta tare da tayar da hankalin mazauna garin.

Ya kara da cewa, a ranar Juma’a da misalin karfe 2 na dare ya samu kiran waya cewa ‘yan bindigar sun far wa kauyukan, ya kuma umarci jami’an tsaro da su garzaya wurin domin dakile harin.

“Idan ba a dauki matakin gaggawa da jami’an tsaro suka dauka ba, girman harin zai yi yawa, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile su, ‘yan bindigar sun gudu kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike,” in ji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa an tattauna lamarin ne a ranar Juma’a a taron majalisar zartarwa ta jihar, inda Gwamna Inuwa Yahaya, ya amince da raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Ya ce tawagar gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamnan ta ziyarci karamar hukumar da safiyar Juma’a domin jajanta musu tare da bayar da kayayyakin tallafin da suka kunshi kayan abinci.