Kasar Morocco ta kafa tarihin zama kasar Afrika ta farko da ta fara kai wa zagayen kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin duniya.
Hakan ya biyo bayan doke tawagar kasar Portugal da ci daya da babu a zagayen kusa dana kusa dana karshe.
Dan wasa El-Naysiri ne ya ci wa Morocco kwallonta da kai a minti na 43 na fara buga wasan.
Duk da cewa kasar Portugal ta kai munanan hare-hare amma har aka tashi ba ta iya farkewa ba, kuma a karshen wasan an bai wa Morocco jan kati dab da a tashi wasa bayan da da dan wasan gaba Ceddari ya karbi jan kati bayan an bashi katin gargadi har sau biyu saboda keta da ya yi.
Idan anjima ne za a fafata wasa tsakanin Ingila da Faransa kuma duk kasar da ta samu nasara za ta kece raini da Morocco.
A yanzu Maroko za ta buga wasan kusa da karshe da duk wanda ya yi nasara tsakanin Faransa da Ingila yau da daddare.