Zan fara nada wa Abuja magajin gari idan na zama shugaban Najeria – Atiku

0
110

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alkawarin ba yankin Babban Birnin Tarayya Abuja matsayin Magajin Gari a maimakon na Minista muddin ya lashe zabe mai zuwa.

Ya ce zai yi hakan ne domin tabbatar da tsaro da kiyaye rayukan mazauna yankin.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin gangamin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a Abuja ranar Asabar, inda ya ce mazauna yankin za su samu dukkan hakkokin da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba su a gwamnatinsa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi wannan alkawarin ne lokacin da yake mayar da martani kan rokon da Sanatan Abuja, Philip Aduda, ya yi masa, inda ya ce mutanen yankin na son gwamnati mai matsayin ta jiha ta kashin kansu, ko da kuwa ba ta kai ta jihar karfi ba.

Atiku ya ce, “Dukkan hakkokinku da ke cikin kundin Tsarin Mulki na yanzu, da dukkan mukaman da ya kamata a ba ku, za mu ba ku. Kun san me muka yi muku a baya, yanzu ma kuma za mu sake yi.”

Dan takarar ya kuma yaba wa mutanen yankin kan irin goyon bayan da ya ce PDP na samu daga wajensu, inda ya ce jam’iyyarsu ba ta wasa da hakan.

Ya ce, “Mun tabbatar za ku goya mana baya kamar yadda kuka saba.