Hakimin da ƴan bindiga suka harba a Zamfara ya mutu

0
140

Hakimin Yankuzo da ke karamar Hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Kogo Hamza, wanda ‘yan bindiga suka harba ya rasu a lokacin da ya ke jinya a asibiti.

Wasu ƴan bindiga ne su ka harbi Hamza a hanyar Tsafe Yankuzo, inda aka garzaya da shi babban asibitin tarayya dake Gusau, inda ya mutu a ranar Asabar.

Yankuzo dai ita ce mahaifar shugaban ƴan fashin daji, Ado Aliero, wanda sojoji su ka bayyana suna nema ruwa a jallo.

Wani dan yankin mai suna Audu Mohammed, ya ce an kai wa hakimin hari ne a hanyar Tsafe Yankuzo ranar Asabar a lokacin da ya ke komawa yankin sa bayan wata ganawa da Sarkin Tsafe.

Mohammed ya ce, “’yan bindigar sun so su yi garkuwa da shi, amma ya ki tsayawa. Suka bi shi suka bude wa motar sa wuta, shi kuma ya samu raunuka daga harbin bindiga.

“An garzaya da shi babban asibitin Tsafe, daga baya kuma aka kai shi asibitin gwamnatin tarayya dake Gusau, inda ya rasu a daren Asabar.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, bai samu jin ta bakinsa ba domin jin ta bakinsa.