EFCC ta kwato Naira biliyan 30 daga hannun Akanta-Janar da aka dakatar

0
88

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a ranar Alhamis, ta ce ya zuwa yanzu ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga ayyukan cin hanci da rashawa da ya dabaibaye babban Akanta Janar na Tarayya (AGF), Idris Ahmed da aka dakatar.

Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a taron manema labarai da tawagar shugaban kasa kan sadarwa ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ku tuna cewa a halin yanzu Hukumar tana tuhumar AGF da ke daure a kai bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.

Da yake bayar da karin haske kan nasarorin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu daga watan Janairu zuwa Disamba, 2022, shugaban na EFCC ya bayar da adadi na wasu kudi da ya kwato N134,33,759,574.25, $121,769,076.30, £21,020.00, €156,925.00, 50.0.00, C50.0,00, da dai sauransu.

Ya kuma bayyana cewa sama da mutane 3,615 aka yanke musu hukunci a cikin wannan lokaci, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin da gaske take kan shirinta na yaki da cin hanci da rashawa.

Ya sanar da cewa, za a yi gwanjon motocin da aka yi watsi da su a fadin kasar tare da jefar da gidaje sama da 150 ga masu sha’awar saye.

Bawa ya tabbatar da cewa, a lokacin da hukumar da ke yaki da safarar kudaden haram (SCMUL) ta fara aiki, zai yi wuya a yi amfani da kudaden haram a kasar nan.