Jakadan Najeriya a kasar Spain Demola Seriki ya rasu

0
75

Jakadan Najeriya a kasar Spain, Demola Seriki, ya rasu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan siyasar na Legas ya rasu ne a birnin Madrid na kasar Spain yana da shekaru 63 a duniya.

An sanar da rasuwarsa ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun ‘ya’yansa a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce ya mutu a birnin Madrid na kasar Spain da sanyin safiyar ranar.