A cewar BBC, wata doka da majalisar dokokin kasar ta zartar a ranar Talata ta ce duk wanda aka haifa bayan shekara ta 2008 ba zai iya siyan taba ko sigari ba.
Sakamakon haka, adadin mutanen da za su iya siyan taba yana raguwa kowace shekara.
Ministar lafiya ta New Zealand Dr. Ayesha Verrall, wacce ta gabatar da kudirin, ta ce wani mataki ne “zuwa makoma mara shan taba”.
Ta ci gaba da cewa, kudirin dokar an yi shi ne don rage yawan masu sayar da taba zuwa 600 a duk fadin kasar, inda ya ragu daga 6,000 a halin yanzu, da kuma rage yawan sinadarin nicotine da ke cikin kayayyakin don rage sha’awar su.
Dubban mutane a kasar za su kara tsawon rai da lafiya, a cewar ministan lafiya.