Ribas: ‘Yan sanda sun tabbatar da harbin wani matashin daraktan matasa na Atiku

0
104

‘Yan sanda a jihar Ribas sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun harbe Rhino Owhorkire, Daraktan Tattalin Arzikin Matasa na Majalisar Kamfen din Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, wadda ta tabbatar da cewa, “Haka ya faru. Na yi magana da jami’in ‘yan sanda na yankin.

“Muna aiki don samun cikakkun bayanai, amma zan iya gaya muku cewa an fara bincike. Za mu je kan tushen lamarin, mu kamo wadanda ke da hannu wajen kai harin, mu tabbatar sun fuskanci shari’a.

Wata majiya ta ruwaito cewa, “Shi (wanda aka azabtar) dan Aluu ne. Jiya da daddare ne ya je gidansa inda wasu da ba a san ko su waye ba suka harbe shi. Suka harbi tayoyin motarsa, suka harbe shi kai tsaye a gaban gilashin motarsa.

“Kuma ta haka ne ya sami raunukan a bakinsa. Bakinsa ya watse. Yayin da nake magana da ku, yana jin zafi sosai. Amma yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.