Kotu ta tsare wani mutum bisa zargin yi wa diyarsa mai shekaru 21 fyade

0
108

Wata Kotun Majistare da ke Iyaganku a Jihar Oyo a ranar Juma’a ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai suna Opeyemi Ajala bisa zargin yi wa diyarsa mai shekaru 21 fyade.

Alkalin kotun, Emmanuel Idowu, bai amsa karar Ajala mai shekaru 40 ba, saboda rashin hurumi.

Idowu ya bada umarnin a tsare Ajala a gidan gyaran hali na Abolongo, cikin garin Oyo.

Ya ce tsare-tsaren yana jiran shawarar shari’a daga hukumar kula da kararrakin jama’a ta jihar Oyo (DPP).

Idowu ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 1 ga watan Fabrairu.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ajala na unguwar Maya Compound, Ogbomoso da laifin fyade guda daya.

A cewar Lauyan masu gabatar da kara, ASP Amos Adewale, Ajala a watan Agusta, a Maya Compound, unguwar Gaa Legbedu, Ogbomoso ya yiwa diyar sa fyade.

Adewale ya ce laifin ya sabawa tanadin sashe na 357 kuma hukuncin da ya dace a karkashin sashe na 358 na dokokin laifuka na jihar Oyo na shekarar 2000.

NAN ta ruwaito cewa idan aka same shi da laifin fyade, za a yi masa hukuncin daurin rai-da-rai.