Asarar da mutane suka yi sakamakon rushe kasuwar Mile a Legas

0
89

‘Yan kasuwa a Kasuwar Mile 12 da Hukumar Cigaban Karamar Hukumar Ikoshi Isheri (LCDA) ta rushe shagunansu a Jihar Legas sun koka kan asarar jarin da suka yi.

Wadanda abin ya shafa rusau a sashin Redbridge na kasuwar sun shaida wa Aminiya ranar Lahadi cewa ba a ba su wata sanarwa ba.

Sun yi zargin cewa shugabar hukumar LCDA ta umurci ‘yan baranda da suka abka cikin yankin tare da jami’an tsaro da su rusa wani sashe na kasuwar.

Wani da lamarin ya shafa, Usman A Salihu, ya ce ya tashi da sanyin safiyar ranar Alhamis, sai ya lura cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin, inda suka kwashe rufin kantuna tare da yin barna.

Ya ce, “Sai kawai muka ga sun cire rufin gine-ginenmu; akasarin mutanen da ke zaune a yankin Hausawa ’yan kasuwa ne daga Arewa.”

Ya ce saboda umurnin da wani tsohon Gwamnan Jihar Legas, Raji Fashola ya ba su, ya ba su shawarar kada su kwana a cikin kasuwar, yawancinsu sun mallaki shaguna a yankin Redbridge inda suka mayar da su gidajen zama inda suka zauna tare da iyalansu.

Wata mata da abin ya shafa mai suna Fatima Afolabi ta ce, “An gaya min cewa wani ya sayi wurin. LCDA sun sayar da yankin da muka mamaye ga wani, kuma ko da haka ne, ya kamata su sanar da mu; kamata ya yi su ba mu lokaci mu kwashe kayanmu daga ginin, amma sai muka tashi muka tarar da ‘yan daba a yankinmu suna lalata mana dukiya.”

Wani wanda abin ya shafa, Abdul’aziz Gbomiwa, wanda ke aiki a cibiyar POS, ya ce barayin sun yi wa shagon sa fashi, kuma ya yi asarar dukiya ta N2m.

Don haka wadanda abin ya shafa sun bukaci a yi adalci a lamarin.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin shugabar kasuwar, da kuma shugabar kungiyar Ikosi Isheri LCDA, ya ci tura.