Kwankwaso ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da APC da PDP

0
104

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP a 2023  babban zaben kasar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a jiya a wata ziyara da ya kai wa Sarkin Jama’a a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a a Kudancin Jihar Kaduna.

Ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai farfado da fannin ilimi tare da tabbatar da cewa yaran da ba sa zuwa makaranta da marasa galihu sun samu hanyar komawa makaranta.

Ya ce, “Na yi shi a jihar Kano kuma a matakin tarayya zan yi. Zan gina azuzuwa 500,000 ga yaran da ba su zuwa makaranta don tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatun firamare kyauta tilas.”

Ya kuma yi alkawarin biyan kudin WAEC da NECO ga dalibai, tare da bayar da tallafin karatu ta atomatik ga daliban da suka fi kwarewa a fannoni daban-daban don yin karatu a ko ina a duniya.