An kashe kasurgumin dan bindiga madaki mansur da wasu 11 a Bauchi

0
103

’Yan sanda sun kashe kasurgumin dan ta’adda Madaki Mansur tare da wasu 11 a wani samame a Dajin Alkaleri da ke Jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya ce Madaki Mansur shi ne dan ta’addan da ya addabi Karamar Hukumar Alkaleri, da makwabtanta jihohin Filato da Gombe.

Wakil ya ce, “A ranar 19 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 02:30 na rana, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kama wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a maboyarsu guda hudu — Mansur, Digare, Gwana da Dajin Madam a dajin Alkaleri.

“’Yan sandan sun kashe 12 daga cikin masu garkuwa da mutane, yayin da wasu kuma aka fatattake su tare da tarwatsa su, inda wasu daga cikinsu suka samu raunuka.

“Sakamakon haka an samu nasarar kwato makamai da babura a samamen,” in ji kakakin.

A baya-bayan nan, bayan gano man fetur a yankin Alkaleri da ke tsakanin jihar Bauchi da Gombe, an ruwaito yadda ’yan bindiga suka addabi al’ummar yankin.

Sai dai rundunar ’yan sanda Jihar Bauchi, ta bayyana rahoton a matsayin labarin kanzon kurege.