Mutanen da aka kashe a harin da aka kai kudancin Kaduna

0
102

A daren Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Malagum 1 da Sokwong da ke masarautar Gworok a karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane kusan 28 tare da jikkata wasu da dama.
Da yake tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, Sakataren Majalisar Karamar Hukumar Kaura, Hon. Raymond Ibrahim ya ce ‘yan bindigar sun fara kai hari a yankin Sakwong ne da misalin karfe 11:58 na dare inda suka kashe mutane 9 tare da kona gidaje da kadarori.
“Mun je wurin da abin ya faru a safiyar yau, mun ga gawarwaki tara da idanunmu. Daga nan ne muka je Malagum 1 inda muka tabbatar daga majiya ta gaskiya cewa a can ma an kashe mutane 19,” inji shi.

Ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyar bayan da aka kai hari a Malagum 1 inda aka kashe mutane hudu. Yayin da yake kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, Hon. Ibrahim ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa jama’arsu domin da yawa daga cikinsu sun zama marasa gida.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Muhammed Jalige, bai amsa kiran wakilinmu ba.