Gidan radion Premier sun koka bisa zargin cin zarafin ma’aikacinsu da ‘yan sanda sukayi

0
112

Gidan Rediyon Firimiya a Kano ya yi Allah wadai da cin zaafn da aka yiwa ma’aikacin gidan rediyon Muhammad Bello Dabai.

An bayyana cewa al’amarin ya faru ne a gaban tashar yayin da ma’aikatan ke gudanar da aikinsa na a ranar Litinin da yamma.

A wata sanarwa da manajan labarai da rahotanni na Premier, Mukhtar Yahaya Usman ya fitar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa bai ce komai ba kan lamarin.

Gidan rediyon Premier ya yi Allah-wadai da mummunan cin zarafin da aka yiwa ma’aikacin gidan rediyon, Muhammad Bello Dabai a gaban tashar yayin da yake gudanar da aikinsa a ranar Litinin da yamma wan da hakan bai sabawa ka’idar aikin jarida ba.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana inda aka kira Muhammad Beelo Dabai domin ya dauko rahoto game da wani barawo da aka kaishi asibitin Nassarawa domin magani ya tsere.

Yayin da jama’a ke bin sa suna jifansa da duwatsu, sai barawon ya karaso  dab da Tashar mu.

Ma’aikatanmu da suka hada da Muhammad Bello Dabai sun kasance a wurin da lamarin ya faru a matsayin shaidu a gaban jami’in ‘yan sanda da ke bakin aiki a ofishinmu da ake kira da Area Command na ‘yan sanda.

Lokacin da ‘yan sandan suka isa wurin domin bada kariya ga mai laifin,  Dabai yana wajan a matsayin dan jarida.

Wani abin mamaki kuma ba tare ma’aikacin mu dabai yace komai ba sai daya daga cikin ‘yan sandan ya tunkare shi don ya hana shi, daukan rahoto.

Ko da Dabai ya nuna masa katin shaidarsa, kuma ya bayyana kansa a matsayin dan jarida, sai dan sandan ya kama shi da karfi, inda ya tura shi cikin motar su ta ‘yan sanda, inda ya bayyana cewa za su kai shi ofishin ‘yan sanda domin yi masa tambayoyi tare da tsare shi.

An yi wa Dabai dukan tsiya tare da mari da dama a kan hanyarsu ta zuwa ofishin, inda kuma aka tilasta masa ya kwanta a ckin motar.